Gwamnatin Tarayya Ta Fara Tura Tallafin Naira ₦50,000 Ga Wanda Suka Cike President Conditional Grant Scheme

Gwamnatin Tarayya (Federal Government) a jiya asabat 10 ga watan Match ta fara bayar da tallafın dubu hamsin #50,000 shirin nan na President Conditional Grant Scheme mutane miliyan daya ne zasu ci gajiyar shirin nan.

An cike wannan tallafin kwanaki, haka kuma mun kawo muku shi cikin wannan website namu mai albarka a kwanakin baya

Sai kuma tallafın ya kasu kashi uku kamar yadda muka sanar a lokacin da muka kawo muku shirin; daya KYAUTA ne biyun kuma duk BASHI ne wato za a biya daya baya; ya danganta da wanda ka cike

  1. Shirin Ba da Tallafin Sharadi na Shugaban Kasa (PCGS)
  2. Asusun shiga tsakani na FGN MSME
  3. FGN Manufacturing Sector Fund.

TSARIN BAYANIN SHARI’AR SHUGABAN KASA (PCGS)

Shi wannan kyauta ne za fitar da shi daga asusun

N50,000,000,000 wanda za a raba naira dubu hamsin hamsi #50,000 ga mutane 1,000 a

kowace karamar hukuma (Local Government.Kyauta ce kuma ba za a biya ba

FGN MSME KUDIN SHIGA (LOAN)

Shi kuma wannan bashi ne ba kyauta za a fitar da shi daga asusun N75,000,000,000, duk wanda ya yi sa’ar samun wannan gajiya zai samu rancan naira miliyan daya #1,000,000 daga cikin mutanen da suke Micro, Small, and Medium Enterprises (MSMEs) za a biya wannan ba kyauta ba ne.

KUDIN SAKAMAKON MANUFACTURING FGN (LOAN)

Wannan ma bashi daga asusu na naira biliyan #75,000,000,000 za a ba masu manyan masana’antu (companies) sannan duk mai cin gajiyar zai samu nera miliyan daya #1,000,000. Bashi ne ba kyauta ba.

Related Post  Yanda Zakayi Nin Verification Na Presidential Conditional Grant Scheme (PCGS).

Na farkon wato THE PRESIDENTIAL CONDITIONAL GRANT SCHEME (PCGS) shi ne kyauta, sannan kuma an fara tura wannan tallafın jiya asabat 10 ga watan Match 2024. Allah Ya mu dace.